Qurani·قرآني
Hausa

Ayatul Kursiyyu: Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye ne, Madauw — Azkar Asuba

آيَةُ الْكُرْسِيِّ: اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
Rubutu da Latin: Ayat al-Kursi: Allaahu laa ilaaha illaa huwal-hayyul-qayyoom...
Fassara: Ayatul Kursiyyu: Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye ne, Madauwami. Gyangyadi ba ya kama Shi, ballantana barci. Ninsa ne abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa. Wane ne wanda zai yi ceto a wurinSa sai da izininSa? Ya san abin da yake gabaninsu da abin da yake bayansu, kuma ba su kewaye da wani abu daga iliminSa ba, sai da abin da Ya so. KursiyyinSa ya yalwaci sammai da kasa, kuma kiyaye su ba ya nauyaya maSa. Shi ne Madaukaki, Mai girma.
Tushe: Quran 2:255
Komawa zuwa rukuni Buɗe a aikace-aikacen Qurani